YADDA ZAKU SHIGA TSARIN iHATCH

 


iHatch 3rd Cohort Registration Form

Ofishin (ONDI) tare da haɗin gwiwar Hukumar Hadin gwiwar Kasa da Kasa ta Japan (JICA) za su ƙaddamar da iHatch.

iHatch wani shiri ne da zai taimakawa masu son fara kasuwanci da kuma wadanda basu dade da farawa ba. Shirin zai ba da kyakkyawar dama ga masu fara kasuwanci waɗanda ke da sababbin tsare-tsaren kasuwanci wato (Plan) tare da samfirin kasuwancin.


iHatch shiri ne mai tsauri na kyauta na watanni 5 wanda aka tsara don taimakawa 'yan kasuwan Najeriya su inganta tunanin kasuwancin su ta hanyar jerin koyawa, lakcoci, da sansanonin samar da samfuran kasuwanci don a samu daidaitawa.


Wadanda suka samu damar shiga shirin zasu mori kayan karatu na zahiri dana online kyauta daga manyan malaman karatun


Za'a yi wannan shirin ne a garuruwa kamar haka:

1 - FCT Abuja

2- Kano

3- Lagas

4- Gombe

5- Rivers


Za'a rufe cike wannan form daga ranar 7/01/2023


Domin yin register sai a shiga nan:

https://forms.office.com/r/ynEzWNEFj6


Idon bai shiga ba sai ayi copy and paste na link din.


Comments

Popular posts from this blog

MENENE DIGITAL MARKETING